Majalisar dattawa ta Dage Muhawarar da ta shirya kan kayyade cirar kudi da CBN yayi

Senate
Senate

Majalisar dattawa ta dage muhawarar da za ta yi kan manufar cirar kudaden da babban bankin Najeriya ya yi har zuwa ranar Laraba 14 ga watan Disamba, 2022.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Larabar da ta gabata ne Majalisar Dattawa ta tsayar da ranar Talata 13 ga watan Disamba, 2022, domin ta tafka muhawara kan manufar Babban Bankin Najeriya kan iyakance fitar da kudade.

Wani mamba a kwamitin, Sanata Olubunmi Adetumbi, a cikin wata sanarwa ya shaida wa abokan aikinsa cewa, rashin halartar shugaban kwamitin kula da harkokin bankuna da kudi, Sanata Uba Sani, wanda ya tafi gangamin taron shugaban kasa na jam’iyyar APC Kaduna.

Adetumbi ya tabbatar wa majalisar dattijai cewa rahoton kwamitin kan manufofin kayyade cirar kudin a shirye yake, inda ya ce dole ne shugaban kwamitin ya halarci taron jam’iyyar APC na shiyyar a matsayinsa na dan takarar gwamnan jihar Kaduna.

Da yake mayar da martani, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi kira ga ‘yan majalisar da su yi hakuri domin za a bayyana sakamakon kwamitin a cikin sa’o’i 24.

Ana kuma sa ran Uba Sani zai yi wa takwarorinsa bayanin sakamakon tantance Edward Adamu da Aisha Ahmad a matsayin mataimakan gwamnonin CBN.

Sai dai kuma wani dan majalisar, Sanata Muhammed Bulkachuwa ya yi gargadin cewa kada majalisar dattawa ta yi watsi da batun a karkashin kafet saboda mahimmancin manufofin, yana mai cewa majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele da ya gurfana a gaban majalisar domin tattaunawa kan lamarin.

A makon da ya gabata ne dai bankin CBN ya fitar da mafi girman cire kudi na yau da kullun ta hanyar ATM da PoS) akan Naira Dubu 20.

Babban bankin na CBN ya ce, wannan sabuwar manufar ta biyo bayan kaddamar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022.

Ta umurci bankunan da su tabbatar da cewa kudaden da mutane da kamfanoni ke cirewa duk mako kada ya wuce Dubu N100 ga kowanne muyum da Naira Dubu 500 ga kamfanoni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here