Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta amince da sake tura manyan hafsoshi 69 zuwa ofisoshin shiyyoyi a fadin kasar nan.
Kwanturola Janar na Hukumar, Mista Isah Jere, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Amos Okpu, ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Sanarwar wadda ke dauke da lamba NIS/HQ/ADM/4423/170 da kwanan watan 1 ga watan Agusta, ta bada umarnin fara aiki nan take.
Sanarwar ta ce, umarnin sauya wuraren aikin ya shafi mataimakan Kwanturola 8 (ACG) da kuma Kwanturolan Shige da Fice (CIS) 61.
Ya ce ACGs da aka tura sun hada da: ACG KM Amao wanda ya kasance Kwanturolan Rundunar Ogun an maida shi Babban Jami’in Tsaro a hedikwatar ma’aikatar dake Abuja.
ACG K.N Nandap, wanda ya taba rike mukamin kwamandan Hukumar a filin tashi da saukar Jiragen Sama na Murtala Mohammed dake Ikeja, a yanzu shi ne Shugaban sashen hadin Kan Kasashen Waje da bada Katin izinin zama a ciki (CERPAC) na hedikwatar.
“Hakazalika, ACG Abdullahi Usman a yanzu shi ne shugaban sashin kula da kaura na yau da kullun a hedkwatar ma’aikata.
“ACG B.N Alawode ya zama shugaban walwala yayin da ACG EC Esedo shi ne mai kula da shiyyar, Zone ‘D’ a Minna, da sauransu” in ji shi.