Rundunar Tsaro ta Farar Hula ta Najeriya (NSCDC), reshen jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar mutane biyar sakamakon wani mummunan hari da aka kai a ƙaramar hukumar Jahun ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar, ASC Badaruddeen Tijjani, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse a ranar Alhamis, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Gurjiya, da ke gundumar Aujari ta ƙaramar hukumar.
Read also: Ambaliyar Ruwa Ta Katse Titin Kano Zuwa Maiduguri
Tijjani ya ce, “NSCDC ta yi Allah-wadai da harin da aka kai a ƙauyen Gurjiya, gundumar Aujara, ƙaramar hukumar Jahun, da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Alhamis, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar da raunata wasu shida.”
Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wasu da ake zargin maharan ne suka kai harin, wanda ake kyautata zaton ramuwar gayya ce dangane da wani rikici da ya faru kimanin watanni biyu da suka gabata.
Mai magana da yawun rundunar ya ƙara da cewa, rikicin da ya gabata ya shafi wasu da ake zargin ɓarayi ne da suka kai hari garin domin yin sata, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu.
Tijjani ya bayyana sunayen waɗanda suka mutu a harin da Abdulmumini Abdullahi, mai shekaru 70, Malam Ashiru, mai shekaru 70, Miko Maigwanjo Duja, mai shekaru 60, Aki Faruq Atman, mai shekaru 45 da Isyaku Imamu, mai shekaru 50.
A cewarsa, wasu mutane shida sun samu raunuka daban-daban, ciki har da sara da makamai da kuma raunukan kibiyoyi.
Read also: Masu amfani da Thread sun kai miliyan 100 a kwana biyar
Ya ce, “Ƙarin bincike ya nuna cewa an tattara mahaya raƙuma sama da 100, tare da wasu mutanen da ba a tantance su ba, waɗanda ake zargin suna da alaƙa da lamarin. Sai dai ana ci gaba da tantance waɗannan rahotanni yayin da bincike ke gudana.
Ya ce Kwamandan NSCDC na jihar, Muhammad Ingawa, ya yi kakkausar suka ga harin, inda ya bayyana asarar rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a matsayin abin takaici kuma abin da ba za a amince da shi ba.
Ingawa ya yi kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, su yi taka-tsantsan, tare da gujewa ɗaukar doka a hannunsu.
Kwamandan ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara ƙaimi wajen inganta zaman lafiya, ƙarfafa tattaunawa da kuma kai rahoton duk wani motsi ko aiki da ake zargi ga jami’an tsaro da suka dace.
“Rundunar tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka mutu, tare da fatan samun sauƙin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.
“NSCDC na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar Jigawa,” in ji shi.
(NAN)













































