Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa da Gwamna a Jihar Kano na Jam’iyyar APC, ya yi watsi da wani ƙorafi da ke neman Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta gudanar da bincike kan zargin katsalandan a hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamitin ya bayyana ƙorafin, wanda aka rubuta ranar 24 ga Nuwamban 2026, aka kuma ce Comrade K. Suleiman daga Malali, Jihar Kaduna, ya miƙa a madadin ƙungiyar Concerned Nigerian Citizens, a matsayin yaudara, mara sahihan hujjoji, kuma ya samo asali ne daga karkatar da ma’anar hirar da gwamnan ya yi da BBC Hausa a baya-bayan nan.
Read also: Hajjin 2024: Rukunin karshe na Alhazan Najeriya sun shirya dawowa gida
A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar Laraba, wadda mai magana da yawun kwamitin na biyu, Hon. Sanusi Kiru ya sanya wa hannu, kwamitin ya ce masu ƙorafin sun rikita neman shugaban ƙasa ya guji katsalandan a shari’a da kuma zargin cewa an yi ƙoƙarin yin tasiri kan hakuncin kotun.
A cewar kwamitin, Gwamna Yusuf ya bayyana a hirar cewa tsohon jagoransa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya umurce shi da ya je wurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da tabbatar masa cewa za su koma APC idan shugaban ƙasar ya guji katsalandan a shari’ar da ta shafi zaɓen gwamnan Kano na 2023, kuma hukuncin ya kasance a gare su.
SolaceBase ta rawaito cewa kwamitin APC ya jaddada cewa neman shugaban ƙasa ya guji katsalandan a shari’a ya yi daidai da ƙa’idar kundin tsarin mulki da ta tanadi raba ikon gwamnati zuwa sassa daban-daban, don haka ba zai iya zama hujjar cewa an yi katsalandan a shari’ar ba.
Read also: Abinda ya kamata ku sani dangane da matsalar ruwa a Kano
Kwamitin ya ƙalubalanci masu ƙorafin da su bayyana sunan duk wani alƙalin Kotun Ƙoli da suke zargin ya shiga tattaunawar, su gabatar da hujjar umarnin da shugaban ƙasa ya bayar ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma su tabbatar da wata tattaunawa, cin hanci, barazana ko matsin lamba da aka yi da nufin yin tasiri kan hukuncin.
Haka kuma, kwamitin ya ce tattaunawar siyasa da sauye-sauyen sheƙa da suka biyo baya ba za su iya tabbatar da cin hanci ko rashawa a ɓangaren shari’a ba, matuƙar babu hujjojin da ke tabbatar da hakan.
Ya kuma yi nuni da zaɓen gwamnan Kano da aka gudanar ranar 18 ga Maris din 2023, inda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Yusuf a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’u 1,019,602, yayin da babban abokin hamayyarsa ya samu ƙuri’u 890,705, abin da ya ba shi tazarar ƙuri’u 128,897.
Haka kuma, ya tuna cewa Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke ranar 12 ga Janairu, 2024, a shari’ar Yusuf Abba Kabir da APC, INEC da NNPP, mai lamba SC/CV/1179/2023, ta yi bayani kan batutuwa da suka haɗa da sahihancin ƙuri’u 165,616 da aka cire da kuma ikon ƙananan kotuna wajen sauraron batutuwan da suka shafi kasancewa mamba a jam’iyyar siyasa.
Read also: Buhari yaki sanya hannu kan sabuwar dokar zabe
A cewar kwamitin, soke hukuncin da ƙananan kotuna suka yanke da Kotun Ƙoli ta yi wani mataki ne da ya dace da ikon ɗaukaka ƙara da kundin tsarin mulki ya ba ta. Ya ƙara da cewa masu ƙorafin ba su nuna wata alaƙa tsakanin dalilan shari’a da kotun ta yi amfani da su wajen yanke hukuncin da zargin katsalandan daga bangaren siyasa ba.












































