Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Kano mai yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Muhuyi Magaji Rimingado, ya karɓi lambar yabo ta Mayor of Peace daga gidauniyar UN-POLAC.
An karrama shi ne bisa ƙoƙarin gwamnatin Kano da rundunar wajen inganta zaman lafiya da tsaro da kuma yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Read also: Sabon ɗan majalisar wakilan Najeriya daga Taraba ya rasu
SolaceBase ta ruwaito cewa an gabatar da lambar yabon ne a bikin cika shekaru 25 da kafuwar gidauniyar, wanda aka gudanar a ranar Laraba, 25 ga Nuwamban 2026, a Transcorp Hilton da ke Abuja, inda Rimingado ya kuma gabatar da jawabi.
Sauran waɗanda aka karrama a wajen bikin sun haɗa da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, Uwargidan Gwamnan Jigawa da Hajiya Salamatu Garba, wadda ta kafa gidauniyar WOFAN.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Muzaffar Lawal, Mataimaki na Musamman ga shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Kano mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, ya fitar ranar Alhamis.
Da yake karɓar lambar yabon, shugaban kwamitin ya gode wa UN-POLAC da abokan hulɗarta na WOFAN, inda ya bayyana karramawar da cewa “ba kofin nasara ba ne, illa nauyin da aka ɗora.”
Read also: FCCPC ta bankado wata kungiya da ke yin sama da fadi a farashin kaya a fadin kasar – Tunji Bello
Ya ce lambar yabon ta wakilci ƙoƙarin mutane da dama, ciki har da jami’an da ke gudanar da samame da sassafe, masu ba da shawara ga iyalan da matsalar ta shafa, Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya bai wa rundunar umarni da ƙarfin siyasa wajen gudanar da ayyukanta da kuma iyayen Kano, musamman mata.
Muhuyi ya shaida wa mahalarta taron cewa Gwamnan Kano ne ya ƙaddamar da rundunar a ranar 22 ga Yulin 2026, wadda ta ƙunshi jami’an NDLEA, ’yan sanda, DSS, Civil Defence, Kwastam, Immigration, hukumar kula da gidajen gyaran hali da sauran jami’an tsaro a jihar.
Ya ce ya zuwa yanzu rundunar ta kama sama da mutane 1,000 da ake zargi, tare da samun hukuncin kotu kan sama da 830 daga cikinsu. Haka kuma, ta kai samame wuraren sayarwa da shan miyagun ƙwayoyi da sauran maboyarsu a Kano, tare da cafke kusan kapsul 4,080,000 na Pregabalin da aka karkatar da su daga hanyar rarrabawa kafin su isa ga matasa.
Haka kuma, ya jaddada cewa “kama mutane kaɗai ba zai samar da zaman lafiya ba,” yana mai cewa kwamitin na ɗaukar mai shan miyagun ƙwayoyi a matsayin wanda matsalar ta shafa da farko.
Read also: Yan bindiga sun kashe amarya da ango a jihar Plateau
Ya ce masu shan miyagun ƙwayoyi a karon farko, waɗanda aka gwada aka tabbatar suna amfani da nau’in ƙwaya guda, ana ba su shawara sannan a mayar da su ga iyayensu, yayin da waɗanda ke buƙatar magani ake tura su cibiyoyin gyaran hali da na jinya.













































