Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki da Tsaftace Kasuwa ta Kasa (FCCPC) ta sanar da gano wata ‘kungiya’ da ke kara farashin kaya da hidima a fadin kasar duk da kokarin da gwamnatin ke yi wajen daidaita farashin.
Da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a taron yini guda kan yadda ake yin sama da fadi a farashin kayayyaki a garin Uyo, Jihar Akwa Ibom, Shugaban Hukumar, Mr. Tunji Bello, ya bayyana cewa binciken hukumar a manyan birane ya gano abubuwan da ke da ban mamaki.
A fannin kaji, Bello ya jaddada yadda wasu manyan ‘yan kasuwa ke yanke farashin da kananan masu noman kaji za su bi, wanda hakan ke da mummunan tasiri ga karamin mai saye.
“Da farko, masu noman kaji kan sayar da day-old chick tsakanin Naira 480 zuwa Naira 590 kuma suna samun riba. Amma da shigowar wasu manyan ‘yan kasuwa guda biyu, komai ya sauya,” in ji shi, yana mai boye sunayensu.
Ya bayyana cewa kamfanonin sun zuba makudan kudade a fannin, inda suka karbe kashi 80 zuwa 90 cikin 100 na kasuwar kaji.
“Wadannan manyan ‘yan kasuwa sun yi amfani da kudaden su wajen kwace kungiyar masu noman kaji, inda suka tilasta sayar da day-old chick a kan Naira 1,350, wanda ya saba da ka’idar tattalin arziki na cewa karin kera ya kamata ya rage farashi,” ya kara da cewa.
Bello ya jaddada cewa wannan rashin gaskiya ne dalilin da yasa farashin ke nan a yadda yake duk da tallafin gwamnati ga fannin kaji.
A cikin shekarar da ta gabata, Ma’aikatar Aikin Gona da Tsaron Abinci ta Tarayya ta ba masu noman kaji tallafin broilers, kwayoyin cutar kaza, abinci, da kudade a cikin shirin tallafi a shiyyoyi shida na kasar.
Haka kuma ya nuna yadda ake yin sama da fadi a bangaren kayan kunshewa, inda ya bayyana wasu manyan ‘yan kasuwa guda biyar da ke shigo da kayayyakin kunshewa a matsayin kungiya da ke hana farashin sauka.
“Su na aiki irin na ‘mafiya’, idan ka yi kokarin tattaunawa da daya, sai ya sanar da sauran don tabbatar da cewa farashin zai tsaya iri daya,” in ji Bello.
Da yake amsa tambaya kan rashin hukunci a kan irin wannan dabi’ar, Bello ya bayyana cewa FCCPC na kokarin tattaunawa da farko a matsayin gwamnatin dimokradiyya, maimakon daukar matakin da zai haifar da tarar makudan kudade da daurin kurkuku.
Ya bukaci al’ummar ‘yan kasuwa a Akwa Ibom su hada kai da FCCPC wajen kawar da irin wannan ta’asa da kuma inganta adalci a kasuwa.
Don rage radadin talauci ga masu amfani da kaya, Bello ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da wasu matakan rage farashin, ciki har da cire haraji kan shigo da abinci, VAT a kan magunguna da kayan aikin lafiya, rage haraji ga masu kasuwanci da sufuri na jama’a, da kuma bayar da rancen gyara motocin su zuwa CNG.
“Adalci ne kawai ‘yan kasuwarmu da ‘yan kasuwar su rabawa masu amfani da kaya amfanin wadannan matakai ta hanyar rage farashin,” in ji Bello.
Wasu daga cikin masu magana a wajen taron sun bayyana damuwarsu kan tsadar gudanar da kasuwanci a Najeriya, musamman yadda farashin ruwa, haraji mai yawa, da kuma karin farashin wuta ke zamewa kalubale ga ‘yan kasuwa.
Tun da farko, Kwamishina mai kula da ayyuka a FCCPC, Dr. Abdullahi Adamu, ya bukaci masu ruwa da tsaki su bayar da shawarwari don magance ayyukan kungiyoyin da ke taka rawa wajen daidaita kasuwar ƙasar.