Rahoton 2024 na Nazarin Mulki da Tabbatar da Gaskiya a Afirka, wanda cibiyar Mo Ibrahim ta wallafa, ya nuna kalubalen mulki da Najeriya ke fuskanta, inda rahoton ya bayyana koma bayan da kasar ta samu a muhimman al’amura na mulki.
Victor Okebe Agi, jami’in hulda da jama’a a Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Tsafta a Fannin Kudade, ya bayyana cewa rahoton ya saka Najeriya a matsayi na 33 daga cikin kasashen Afirka 53, tare da maki 45.7 daga cikin 100, saukar da darajar ta da maki -1.4 tun daga shekarar 2014.
Akwai kasawa sosai a bangarori masu muhimmanci, irin su Tsaro, Bin Doka (39.7), Hakkoki da Kunshewar Jama’a (47.9), Tushen Dama ta Tattalin Arziki (48.6), da Kuma Ci Gaban Dan Adam (46.4).
Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Tsafta ta sake bayyana cewa sakamakon ya nuna matsalolin mulki da ke cikin manyan hukumomi, jihohi, da kananan hukumomi.
Wadannan bayanai sun nuna matsalolin da ke cikin tsarin mulki baki daya da kuma saukar da darajar Najeriya a Afirka da duniya baki daya.
Rahoton ya gargadi Najeriya game da matsalolin rashin gaskiya, rashin amincin aikin gwamnati, da gazawar daukar matakan yaki da cin hanci da rashawa, wanda hakan ke kawo tasiri mai yawa.
“Saukar da darajar mulkin Najeriya ba wai kawai yana shafar tsaro da zaman lafiya ba, har ma yana hana zuba jari daga kasashen waje da kuma hana bunkasar tattalin arziki,” in ji rahoton, yana mai jaddada bukatar daukar matakai na gaggawa.
Cibiyar ta yi kira ga gwamnati da ta magance wadannan matsaloli ta hanyar karfafa hanyoyin yaki da cin hanci, inganta bin dokokin da aka kafa a cikin dokar Procurement, da kuma samar da kariya mai karfi ga masu tona asiri.
Haka kuma, samar da gyare-gyaren shari’a da tallafa wa manufofin da ke tabbatar da adalci ga kowa na da matukar muhimmanci wajen dawo da amincewar jama’a da tabbatar da doka.
Rahoton ya karkare da kiran da a kara zuba jari a fannin kiwon lafiya, ilimi, da horar da kwarewa, domin gina dan Adam wanda zai iya jagorantar ci gaban tattalin arzikin Najeriya da samun gogewa tsakanin kasashen Afirka.