Tinubu ya gana da manyan malaman Musulunci a kan rikicin Nijar

Islamic Clerics 750x430
Islamic Clerics 750x430

A jiya Laraba ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin tawagar manyan malaman Musulunci na ƙasa, karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Bauchi, inda suka amince da shiga tsakani a rikicin Nijar.

Shugabannin sun je fadar shugaban kasa ne domin tattaunawa da shugaban kasar kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.

A ranar Talatar ne shugaban kasar ya bayyana cewa, har yanzu a bude kofofin sulhu su ke domin ganin an shawo kan rikicin siyasar Nijar cikin ruwan sanyi.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Sheikh Bala Lau, ya ce tawagar ta yi alkawarin samar da mafita mai dorewa a makwabciyar kasar Nijar.

“Tawagar Ulamah a nan Najeriya, ta gana da shugaban kasa kan batun Jamhuriyar Nijar. Muna son samun mafita mai dorewa. Muna son zaman lafiya ba a Najeriya kadai ba, har ma a yankin kudu da hamadar Sahara da ma duniya baki daya.

“Don haka, dukkan Malamai suka shawarci shugaban kasa, cewa muna son zaman lafiya da sulhu.

“Ko da yaushe idan akwai wani abu da ya faru tsakanin ku da makwabcinku, Alkur’ani mai girma ya umurce ku da ku sasanta. Don haka, muna son sulhu.

“Shi ya sa muka zo nan kuma shugabanmu mai ƙwazo ya karɓi tayin cewa yana son mu shiga tsakani kuma mu tattauna da ’yan’uwanmu na can Jamhuriyar Nijar, malamai da kuma yadda za mu taru don samar da mafita mai ɗorewa. wannan matsalar,” Lau ya bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here