Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Sanata Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, ya yaba wa shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu kan matakin da ya dauka na kai karar gwamnatocin jihohin kasar nan a kan rashin samun ci gaba a kananan hukumomi.
Sanata Sumaila a wata sanarwa da ya fitar yace talakawan Najeriya na matukar bukatar manufofin da za su rage musu radadin da suke ciki.
Sumaila ya kara da cewa, shugaba Tinubu ya cancanci yabo domin matakin da ya dauka na tabbatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi ya yi daidai da yadda ‘yan majalisar dattawa suka tsaya a kan kokarinsu na ceto talakawa daga mawuyacin halin da suke ciki.
Karin labari: NMA: ta umarci likitocin asibitin yara na Hasiya Bayero da su janye ayyukansu saboda rashin tsaro a Kano
“Na yi farin ciki, mai girma shugaban kasa ya fara tafiya a kan hanyarmu ta ceto al’ummarmu ta hanyar bai wa kananan hukumomi ‘yancin gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
“Matakin tilastawa jihohi 36 na tarayyar kasar nan na bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu wani mataki ne na tabbatar da gaskiya.
“Hakika hakan zai taimaka wajen kawo ci gaba ga jama’armu, musamman ma mazauna karkara. Hakazalika za ta bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar kara kudaden shiga da ake samu a cikin gida ta hanyar sarkar darajar noma da sauran ayyukan kasuwanci da za su taso bayan kananan hukumomi sun samu ‘yancin cin gashin kansu”.
Karin labari: Gwamnan Kano ya nada mukaddashin manajan daraktan ARTV
Sanata Sumaila, ya roki shugaba Tinubu da ya duba matsalar zaben kananan hukumomi, domin a cewarsa wata matsala ce da ke shafar ci gaban talakawa a karkashin mulkin dimokradiyya.
“Zan yi farin ciki idan har shugaba Tinubu zai magance matsalolin da suka shafi gudanar da zabukan kananan hukumomi a kasar nan. Ya kamata shugaban kasa ya yi wani abu da zai hana ‘yan siyasa yin katsalandan a harkokin zaben kananan hukumomi domin biyan bukatun kansu.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Kotu ta hana Aminu Ado Bayero da wasu mutane 4 gabatar da kansu a matsayin sarakuna
Sanata Sumaila ya tabbatar da cewa ‘yan majalisar dokoki da na zartaswa sun yi nasu bangaren, yanzu ya rage ga bangaren shari’a da su yi amfani da ‘yancinsu na tsarin mulki yadda ya kamata wajen yanke hukunci a shari’ar da ke gabanta kan ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi.
“Mu a Majalisar Dokoki ta kasa mun tabo batun, mun goyi bayan cin gashin kan kananan hukumomi, haka nan ma bangaren zartarwa ya kawo mana hujja. Yanzu ya rage ga bangaren shari’a don tsayawa tsayin daka.
“Na godewa Shugaban Majalisar Dattawa, Mista Godswill Akpabio da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin da suka ba ni damar gabatar da lamarin a gaban Majalisar Dattawa da takwarorina da suka bani goyon baya kan wannan batu,” in ji sanarwar.