INEC ta nemi sifeton ƴan sanda ya yi bincike kan Huɗu Ari

341851562 762516038734392 4353123176730502122 n
341851562 762516038734392 4353123176730502122 n

Hukumar zaɓen Najjeriya ta gudanar da wata ganawa yau Talata a Abuja, inda ta tattauna kan batun zaɓen gwamnan jihar Adamawa da aka karasa a karshen mako.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta rubuta wa sifeton ƴan sanda da ya gudanar da bincike da kuma yiwuwar gurfanar kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, Barrister Hudu Ari.

INEC ta nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya jawo hankalin hukuma kan abin da kwamishinan zaɓen ya aikata domin ɗaukar mataki.

Ta kuma ce baturen zaɓen gwamnan jihar zai ayyana lokacin da ya dace a koma domin ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here