Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Majalisar dattijai ta amince da kudirin dokar wakar kasa a 2024 domin komawa tsohuwar wakar kasa.
Kudirin wanda ya yi gaggawar wucewa karatu na daya da na biyu a ranar Alhamis, yanzu haka yana jiran amincewar shugaban kasa Bola Tinubu.
Majalisar dattijai ta zartar da dokar sauya wakar kasa daga “Tashi, Ya ku ‘yan uwa” zuwa “Nigeria, Mun gaishe ku.”
Tsohuwar wakar da aka yi a lokacin da Najeriya ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba, 1960, za ta maye gurbin wakar da ake yi a yanzu.
Karin labari: Kananun Hukumomi: Sanatan Kano Kawu Sumaila ya yabawa Shugaba Tinubu
Kudirin na neman farfado da wakar da aka yi watsi da ita a shekarar 1978 a lokacin gwamnatin mulkin soja ta Olusegun Obasanjo.
Shugaban Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele ya jaddada tasirin wakar, “bayan an fitar da shi, ya karfafa kishin kasa a tsakanin ‘yan Najeriya.
Waɗanda suka rayu a wancan zamani sun fahimci muhimmiyar rawar da take takawa a tarihin al’ummarmu, suna haifar da ɓacin rai da abubuwan tunawa masu daɗi na shekarunmu na farko” in ji shi.
Karin bayani na tafe…