
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Majalisar dattijai ta yi afuwa tare da kiran Sanata Abdul Ahmed Ningi da aka dakatar a ranar 12 ga watan Maris, 2024, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
An fara kiran ne bayan wani kudiri da mataimakin shugaban marasa rinjaye Sanata Abba Moro ya gabatar, wanda ya nuna nadama a madadin Sanatan da aka dakatar.
Sanata Abba Moro ya yi alkawarin daukar cikakken alhakin abin da Ningi ya aikata, tare da amincewa da tsananin dakatarwar.
Karin labari: Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta amince da dokar komawa tsohuwar wakar kasa
Halin da Sanatan ya yi a lokacin dakatarwar ya kasance abin dubawa da muhawara a cikin majalisar.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya jaddada basirar sanatan tare da bayyana shi a matsayin dan majalisar dattijai mai kima, inda ya kara da cewa matakin kiran Sanata Ningi ya wuce rarrabuwar kawuna na addini da kabilanci.
Cikakken bayanin na tafe…











































