Kungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya sun shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar farawa daga yau Laraba zuwa ranar litinin 22 ga wannan watan.
Likitocin dai sun ce suna neman gwamnatin Najeriya ta biya musu bukatunsu ciki har da inganta yanayin aiki da biyan kuɗaɗen alawus-alawus da ma albashinsu.
A ziyara da wakilin BBC ya kai asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce ya ga marasa lafiya sun cika makil kasancewar wurin ne ake duba marasa lafiya saboda yajin aikin.
Ya ce fuskokin da dama daga cikinsu na cike da damuwa, abin da ke nuna cewa yajin aikin na kwanaki biyar ya fara tasiri.
Wani mara lafiya ya shaida masa cewa ya zo ne daga jihar Gombe don a duba dan uwansa, amma tun safe ba su kai ga ganin likita ba. Likitocin masu neman kwarewa sun shiga yajin aikin saboda a cewarsu gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu ciki har da inganta albashi.
Dakta Abubakar Nagoma Usman, shugaban kungiyar likitocin na arewa maso yamma, ya ce bayan kwana biyar za su koma bakin aiki, sannan su kira taron kungiyar na ƙasa, inda za a bibiyi inda aka kwana tare da ɗaukar mataki na gaba idan gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba.
Marasa lafiya da waɗanda suke kula da su tuni suka fara ficewa daga asibitin don zuwa wani wurin da walau su biya kuɗi a duba su ko kuma asibitin gwamnatin jiha.
Ba wannan ne karon farko ba da likitoci masu neman kwarewa ke shiga yajin aiki, ko a 2021 ma, sau huɗu cikin shekara guda likitocin na yajin aiki, a wani mataki na matsawa mahukunta lamba don su biya musu bukatunsu.
Wannan batu na yajin aikin dai akasari marasa lafiya ne ke shiga tasku kasancewar babu isassun likitoci da za su duba su.













































