Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci Gaba (CITAD) ta nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa ana yi wa mai sharhi a kafafen sada zumunta, Abdul Turaki, barazanar kashe shi sakamakon kalaman da ya yi a bainar jama’a kan zargin wasu harkokin siyasa a jam’iyyar APC mai mulki.
A cikin wata sanarwa da Daraktan zartarwa na CITAD, YZ Ya’u, ya fitar a ranar Alhamis, cibiyar ta ce yunƙurin tsoratar da mutane domin su janye kalamansu ta hanyar barazanar da tashin hankali abu ne da ba za a amince da shi ba.
Read also: An tsaurara Tsaro Yayin Da Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa Zata Yanke Hukunci A Yau
Cibiyar ta bayyana cewa irin wannan mataki na tauye ‘yancin al’umma na bayyana ra’ayoyinsu, yin tambayoyi kan al’amuran siyasa da kuma shiga cikin harkokin gwamnati ba tare da fargaba ba.
“Kashe mai sharhi kan siyasa a Kano, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a watan Satumban 2026, ya sa wannan lamari ya zama abin damuwa matuƙa. Mutuwarsa ya kamata ta zama tunatarwa ga jami’an tsaro cewa bai kamata a yi watsi da barazanar da ake yi wa mutanen da ke bayyana ra’ayoyinsu ba,” in ji sanarwar.
Read also: Kotu ta kori karar neman tsige Shugaban Hukumar EFCC, Olukoyede
CITAD ta buƙaci rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike cikin gaggawa kuma a bayyane kan barazanar da ake yi wa Turaki, gano waɗanda ke da hannu a ciki, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana cutar da shi.
Haka kuma, cibiyar ta yi kira ga hukumomi da su tabbatar ana magance saɓanin siyasa da suka shafi suka ko ra’ayoyin jama’a ta hanyoyin da doka da tsarin dimokuraɗiyya suka tanada, maimakon amfani da tsoratarwa da tashin hankali.
Read also: Shettima ya gargadi shugaban hukumar NAHCON a kan yin aiki shi ɗaya tilo
CITAD ta jaddada cewa ba za a bar lafiyar Abdul Turaki a cikin rashin tabbas ba.













































