Babban Bankin Najeriya ya ƙaddamar da kuɗin eNaira, bankuna 33 sun shiga tsarin

eNaira 1
eNaira 1

Babban Bankin Najeriya ya ce ya kaddamar da kudin dijital wato eNaira inda ya sanya Bankunan 33 a cikin wadanda za su yi harkar ta eNaira tare da N500m.

Gwamnan Babban Bankin CBN, Mista Godwin Emefiele, ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin bikin kaddamar da kudin dijita na CBN, wanda aka fi sani da eNaira, a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

A cewarsa, kaddamar da eNaira nasara ce a aikin bincike da Babban Bankin Najeriya ke yi don ciyar da hada-hadar biyan kudi gaba da kuma sauƙaƙe mu’amalar kuɗi ga al’umma.

Ya ce biyo bayan matsaya da masu ruwa da tsaki da suka hada da bankin banki, ‘yan kasuwa da bukatun yan Najeriya, CBN ta kaddamar da kudin dijital.

Emefiele ya ce eNaira na nuna babban ci gaba a sauyin kudi a Najeriya.

Ya ce ya zuwa yanzu, an ba da N200m ga cibiyoyin hada -hadar kudi, yayin da sama da abokan ciniki 2,000 ke cikin tsarin.

A cewarsa, sama da ‘yan kasuwa 120 sun yi nasarar yin rijista da kudin eNaira.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here