Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna jimami kan rasuwar Engr. Ahmad Ishaq Bunkure, sabon Mai Bada Shawara kan Harkokin Ayyuka, wanda ya rasu ranar Talata a Masar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikansa kuma Ya ba iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.
Rasuwar Engr. Bunkure, kwana daya bayan nadin mukaminsa, ta girgiza mutane da dama, inda aka samu ta’aziyya daga fitattun mutane, ciki har da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauran jami’an gwamnatin jihar.