Tinubu ya nemi majalisar dattawa ta tantance sabbin shugabannin hafsoshin tsaro

tinubu 2

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya aika wasiƙa zuwa majalisar dattawa domin neman tantancewa da kuma tabbatar da sabbin shugabannin hafsoshin tsaro da aka naɗa.

Wasiƙar shugaban ƙasar an karanta ta ne a zauren majalisar dattawa ranar Talata ta hannun shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.

A cewar wasiƙar, sabbin hafsoshin sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede da Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Manjo Janar Waheedi Shaibu da Babban Hafsan Rundunar Ruwa, Rear Admiral Idi Abbas daBabban Hafsan Rundunar Sama, Air Vice Marshal Kennedy Aneke da kuma Babban Hafsan Leken Asiri na Tsaro, Manjo Janar Emmanuel Undiendeye.

Bayan haka, Sanata Akpabio ya mika sunayen wadanda aka naɗa ga kwamitin gaba ɗaya na majalisar domin gudanar da tantancewa da tabbatarwa a mako mai zuwa.

Cikakken labarin na nan tafe…….

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here