Mata Ta Kai Mijin Ta Kotu Saboda Rashin Kaita Saudiyya

Court Gavel
Court Gavel

Wata mata ‘yar shekara 45, Karima Nuhu ta maka mijinta, Musa Falalu, a gaban wata kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa, Kaduna, bisa zargin kin kai ta kasar Saudiyya.

Mai shigar da karar da ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ta shaida wa kotu cewa ta yi aure da Falalu tsawon shekara hudu inda tace ya ba ta abinci ne kawai na tsawon wata biyu kacal.

“Ya shaida min cewa ya rasa aikinsa na tukin mota direba amma ya samu wani a Saudiyya, inda ya bukace ni da in yi hakuri yayin da ya yi alkawarin dauke ni zuwa garesa.

“Ya zuwa yanzu, ina ciyar da kaina. Har ma aro masa kudi domin ya samu kudin tafiyar, amma bayan samun abin da yake so sai ya sake ni,” inji ta.

Matar ta shaida wa kotun cewa ba ta da wani shaida sai Allah da zai hukunta su a ranar karshe.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta zargin yana mai cewa ba gaskiya bane.

Alkalin kotun, Malam Anas Khalifa, wanda ya tabbatar da rabuwar aure tsakanin ma’auratan, ya ce kotun za ta saurari karar ne kawai idan ta na da shaidu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here