Majalisar Wakilai ta Najeriya ta yi watsi da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kara wa’adin zuwashekarau shida ga shugaban kasa da gwamnonin jihohi.
A zaman majalisar na ranar Alhamis, kudirin da Ikeagwuonu Ugochinyere daga Jihar Imo tare da wasu ‘yan majalisa 33 suka gabatar, an shirya karanta shi karo na biyu amma aka yi watsi da shi cikin gaggawa.
Kudirin ya kuma bayar da shawarar cewa a raba iko tsakanin shiyyoyin siyasa guda shida na kasa domin inganta adalci da rage korafe-korafen neman kafa sabbin jihohi.
An ba da shawarar gyara Sashe na 3 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin amincewa da rabon shiyyoyin siyasa na Najeriya a hukumance.
Haka kuma, kudirin ya bukaci kafa mukamai biyu na mataimakan shugaban kasa – daya daga yankin kudu, daya kuma daga yankin arewa.
Har ila yau, an bada shawarar hada ranar gudanar da zabuka, daga na shugaban kasa da gwamna zuwa na majalisun dokoki na jiha da na tarayya da kananan hukumomi.
Bayan an gabatar da kudirin, Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya bukaci jin ra’ayin mambobin ta hanyar kada kuri’ar murya. Amma “a’a” sun fi yawa fiye da “eh,” wanda ya sa aka yi watsi da kudirin.