Uwargidan shugaban kasa ta ziyarci jaririn farko na shekarar 2024 a Abuja

IMG 20240101 WA0007
IMG 20240101 WA0007

Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta ziyarci jaririn farko na bana a Abuja, Boluwatife Johnson.
An haifi jaririn ne da karfe 12.03 na safiyar ranar Litinin a babban asibitin kasa na Abuja.
Uwargidan shugaban kasar ta kuma ziyarci wasu jariran da aka haifa a asibitin, inda ta ba da kyaututtuka ga jariran. A cikinsu akwai tagwaye wadanda aka haife su hade da juna.

Uwar gidan Tinubun ta samu rakiyar matar mataimakin shugaban kasa, Nana Shettima, ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye, uwargidan ministan ayyuka, Umahi, da uwargidan karamar ministar tsaro.

A yayin ziyarar, uwargidan shugaban kasar ta shawarci iyaye mata masu juna biyu da su ba da fifiko ga lafiyarsu.

Kano: Gwamna Yusuf da mataimakinsa sun gudanar da bikin sabuwar shekara ta 2024
“Ina kira ga iyaye mata masu shayarwa da su kula da jariransu yadda ya kamata, su tabbatar da an yi musu riga-kafi yadda ya kamata, su rika shayar da jarirai nonon uwa zalla, tare da samar musu da isasshen abinci mai gina jiki”

Uwar gidan Tinubu ta ce gidauniyarta, Renewed Hope Initiative (RHI), tana aiki tare da haɗin gwiwar UNICEF don ganin an yi wa duk waɗanda aka haifa a Najeriya rajista don tabbatar da ’yancin da kare dukkan yara.

Yan-sanda suna bincike akan sace shugaban karamar hukuma a Nasarawa

Ta ce RHI za ta ba da taimako domin raba tagwayen da a haifa a hade da junan su.

Shugaban asibitin, Mohammed Mahmood, wanda farfesa ne, ya mika godiyar ga matar shugana kasar bisa karamci da take nuna wa asibitin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here