Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ma’aikatan lafiya da suka hada da mambobin kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa wato (NARD) da su koma bakin aikin su.
Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a yayin ganawa da mambobin kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) a fadar gwamnati da ke Abuja.
Shugaban ya bukaci sauran masu tunanin tsunduma yajin aikin da su bi matakin sasanta batutuwan ta hanyar tattaunawa, komai tsawon lokacin da za a dauka.
Karanta Wannan: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum Biyu Bisa Zargin Leken Asiri Ga ‘Yan Bindiga a Katsina
Mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya ce “Bashin da ake bin ma’aikatan lafiya da gaske za a warware.”
“Wannan gwamnatin tana da kyakkyawan tarihi na biyan duk basussukan da ake bin ma’aikatan gwamnati,‘ yan fansho, da ‘yan kwangila kuma har ma mun sake duba basussukan da gwamnatocin baya suka bari, da zarar an kammala tantancewar.
“Na samu labarin cewa wasu daga cikin bukatu 12 da ake bukata domin janye yajin aikin da ake yi tuni an magance su, duk da cewa ba a yi cikakken nazari game da sabon alawus na maáikatan lafiyan ba saboda.”
Shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa za a warware duk wasu bukatun da likitocin ke nema, bayan tantancewa, inda ya dage cewa yajin aikin ba wani abu bane da za a yi la’akari da shi.
Shugaba Buhari ya kuma yaba da rawar da NMA ta taka a matsayin babbar kungiyar likitocin kwararru a Najeriya, musamman dangane da yadda ayyukan su ke gudana.
Karanta Wannan:Shugaban Hukumar Shige Da Fice, Babandede Ya Yi Ritaya
A nasa jawabin, Shugaban NMA, Farfesa Innocent Ujah, ya godewa Shugaban kasa kan nadin mambobi a cikin manyan mukamai a cikin gwamnati.
Ya ce kungiyar ta damu da yajin aikin da likitoci ke yi kuma tana yin iya bakin kokarinta don rage wahalhalun marasa lafiya a fadin kasar tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa.
Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, wanda shi ma ya kasance a wurin taron, ya ce NMA ta kasance tana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa bangaren kiwon lafiya, musamman wajen magance annoba, da kare lafiyar jama’a.













































