Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya wato Immigration, CG Muhammad Babandede, ya yi ritaya daga aiki bayan ya shafe shekaru 36.
A wani zaman da aka shirya don girmama shi a ranar Juma’a, Babandede ya ce a kamala aikin sa a hukumar fiye da yadda ya same ta.
“Na bar hukumar Immigration fiye da yadda na same ta.”
Babandede ya ce ya sami nasarori sosai sakamakon goyon bayan da ya samu daga ma’aikatan sa.
Ya yi kira ga wanda zai gaje shi da kada ya “jefar da tsarin da ake kai”.
A cewarsa, “A cigaba da kyawawan abubuwa sannan a yi watsi marasa kyau.”
Karanta Wannan:BUK Ta Karawa Malamai 27 Girma Zuwa Matsayin Farfesa, Wasu 40 Zuwa Mataimakin Farfesa
Babandede, wanda ya yi alkawarin zama jakada na gari ga hukumar ta NIS, ya ce a koda yaushe zai kasance cikin shiri don taimakawa a duk lokacin da hukumar ta bukace shi.
CG mai ritaya ya shafe shekaru biyar da watanni hudu a matsayin Kwanturola Janar na hukumar.
Mataimakin Babban Kwanturola Janar mai kula da sashin Kudi, Idris Isah Jere, zai fara aiki a matsayin mukaddashin shugaban hukumar har zuwa lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari zai nada wani Babban Kwanturola Janar din.













































