Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta ce ta ceto sarkin Wawa da aka sace a karamar hukumar Borgu ta Jihar Niger.
Wasu mahara dauke da muggan makamai sun yi garkuwa da Dr. Mahmud Aliyu, a ranar Lahadi a fadarsa da misalin karfe 10 na dare.
Karanta Wannan:‘Yan Sanda Sun Kama Mutum Biyu Bisa Zargin Leken Asiri Ga ‘Yan Bindiga a Katsina
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP. Wasiu Abiodun, ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Minna a ranar Asabar.
Abiodun ya ce an kubutar da basaraken ne a ranar Juma’a da misalin karfe 7:30 na yamma, bayan kokarin ‘yan sanda da sojoji da’ yan banga.
A halin yanzu Dr. Aliyu yana samun kulawar likitoci a wani wurin da ba a bayyana ba. (NAN)