Wani dalibi dan shekara 23 dake karatu a kwalejin kimiyya da kere-kere ta Auchi Polytechnic ya kashe kansa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa an sami gawar dalibin dake ajin farko (ND 1) dake karatu a sashin koyon mulki yana rataye daga rufin ɗakin sa a daren Juma’a.
An ce ya bar wata takarda kafin ya kashe kansa daga bisani.
A cewar wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta, ya ba da umarnin a baiwa wata mai suna Sandra wayar salularsa wanda ya nemi gafara daga wajenta a cikin wasikar.
Majiyar ta ce Sandra budurwarsa ce kuma sun kasance ýan aji daya.
“Solomon yana aji a ranar Juma’a kuma ya tafi gida bayan an tashi. Mun dawo gida da yamma ne kawai muka same shi ya rataye kansa.
Karanta Wannan:‘Yan Sanda Sun Ceto Basaraken Da Aka Yi Garkuwa Da Shi a Jihar Niger
A cewar majiyar “Yaro ne mai kawaici wanda ya dauki malamansa da muhimmanci.
Ba ya fita kuma bai taba nuna alamar bacin rai ba, ” in ji majiyar.
Kakakin kwalejin, Mista Mustapha Oshiobugie, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce har yanzu ba a yi masa cikakken bayani ba. (NAN)












































