Gwamnan Kano ya aike da suna daya zuwa majalisar dokoki domin tantance shi a matsayin kwamishina

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya mika suna guda daya ga majalisar dokokin jihar domin tantance shi a matsayin kwamishina.

Kakakin majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Litinin a lokacin da yake karanta wata wasikar gwamnan mai dauke da sunan Ibrahim Yakubu Adamu.

Ya ce wanda aka nada Ibrahim Yakubu Adamu a halin yanzu shi ne Manajan daraktan hukumar tsare-tsare da Clcigaban Birane ta jihar Kano (KNUPDA).

Falgore ya ce nan ba da jimawa ba za a gayyaci wanda aka bada sunan sunan sa zuwa gaban majalisar domin tantance shi.

Karanta: Gwamnan Jigawa ya dakatar da kwamishina bisa zargin mu’amala da matar aure

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa majalisar ta kuma zartas da wani kudiri a ranar Litinin din na kafa hukumar kula da ababen more rayuwa.

Shugaban masu rinjaye, Lawan Husseini na jam’iyyar NNPP mai wakiltar karamar hukumar Dala ya ce hukumar za ta inganta gudanarwa da kuma kula da kayayyakin more rayuwa a jihar.

Husseini ya kara da cewa hukumar za ta daidaita tsare-tsare, bunkasawa da kuma kula da muhimman ababen more rayuwa a fadin jihar, kamar tituna, gadoji da gine-ginen jama’a.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here