Alkalin Alkalan Najeriya ya yi murabus

Ibrahim Tanko Muhammad
Ibrahim Tanko Muhammad

Shugaban Alkalan Najeriya, Justice Tanko Muhammad, ya yi murabus daga kujerar sa.

Channels Tv ta ruwaito cewa Alkali Tanko Mohammad ya yi murabus ranar Litinin kuma yace ya ajiye aikinsa ne sakamakon rashin lafiya. Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ana shirin nada Justice Olukayode Ariwoola, matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa za’a sanar da murabus dinsa nan ba da dadewa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here