Hukumar Kwastam ta ƙasa ta bayyana cewa za a fara gudanar da gwajin miyagun ƙwayoyi a matsayin dole ga dukkan sabbin jami’ai da kuma ma’aikatan da ke ci gaba da aiki domin tabbatar da ingancin ɗabi’a da kare tsaro a hukumar.
Shugaban hukumar, Adewale Adeniyi, ya sanar da sabon matakin ne a wajen rufe taron shugaban hukumar na shekara ta 2025 da aka gudanar a birnin Abuja, inda ya bayyana cewa gwajin ya zama muhimmin ɓangare na tsarin ɗaukar ma’aikata na wannan shekara.
Ya ce matakin ya na da nufin hana shigar sabbin jami’ai masu halaye mai kyau ba masu amfani da miyagun ƙwayoyi ba, domin irin wannan hali kan iya lalata matakin yanke hukunci, rage tsaro da kawo cikas ga ingantaccen gudanar da ayyukan hukumar.
Adeniyi ya bayyana cewa duk da cewa matakin ya fi karkata ga sabbin ma’aikata, zai shafi dukkan ma’aikata a hedikwata, sassa da rundunonin hukumar, domin tabbatar da kafa cikakkiyar hukumar da ba ta da alaƙa da shaye-shaye.
Ya ce an sha samun matsalolin rashin daidaiton hali da yanke hukunci mara kyau a wasu sassa, wanda daga baya akan gano ya samo asali ne daga amfani da miyagun ƙwayoyi, don haka babu wani sassauci a wannan sabon tsarin.
Ya jaddada cewa hukumar za ta tabbatar da gwajin ga dukkan jami’ai domin kaucewa kashe kuɗaɗe wajen gyara halayen ma’aikatan da ke fama da shaye-shaye, tare da tabbatar da cewa duk wanda ke cikin hukumar ya kasance cikin ingantacciyar koshin lafiya.













































