Harin jirgin ƙasa na Kaduna: Shugaban ƴan ta’adda ya bai wa Tukur Mamu Naira Miliyan 50 daga cikin kuɗin fansa – Binciken DSS

Alhaji Tukur Mamu 750x430

Wani binciken hukumar tsaron ta DSS ya shaidawa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa, shugaban ƙungiyar ’yan ta’adda da suka kai harin jirgin ƙasa tsakanin Abuja da Kaduna a shekarar 2022 ya bai wa Tukur Mamu rabonsa a cikin kudin fansa na Naira Miliyan Hamsin.

Jami’in DSS, wanda ya bayar da shaida a matsayin mai gabatar da kara na 6 (PW-6) a ci gaba da shari’ar ta’addancin da ake yi wa Mamu, wanda ake zargi da tattaunawa ‘yan ta’addan, ya shaida wa mai shari’a Mohammed Umar yayin da lauyan DSS, David Kaswe ke jagoranta a gaban kotu.

Jami’in ya bayyana wa mai shari’a cewa hulɗar da aka samu ta murya daga na’urorin Mamu ta nuna cewa ƙungiyar ’yan ta’addan ta nemi taimakon sa wajen koyar da su yadda ake buɗe shafin internet domin gudanar da ayyukansu, tare da tantance ranar isar da kudin fansa.

Shaidar ta kara bayyana cewa bayan kama Mamu a ƙasar Masar, na’urorin sa da suka haɗa da kwamfuta korar Samsung da wayoyi biyu an mika su ga sashen bincike na DSS, inda daga ciki aka fito da bayanan zantukan sa da ’yan ta’addan, ciki har da sakonnin murya da suka tabbatar da tattaunawar su game da kudin fansa da bukatun ƙungiyar.

Bayan dawowar Mamu Najeriya, jami’an bincike sun gudanar da aikin bincike a gidansa da ofishinsa a Kaduna, inda suka gano kuɗaɗen ƙasashe da na cikin gida, da kuma motocin da suka haɗa da nau’o’in Toyota Camry, Peugeot, Lexus, Mercedes E350 da Hyundai, wadanda a cewar shaidar, wadanda suke tare da shi sun kwashe su zuwa wasu wurare bisa umarnin sa kafin dawowar sa.

Jami’in ya ce Mamu ya amince da cewa ya yi hulɗa da ’yan ta’addan ta hanyar sakonnin murya, ya kuma amince cewa ya umurci wani dangi nasa mai suna Mubarak Tinja da ya fitar da kayayyaki daga gidansa domin kauce wa gano su, kuma ya tabbatar da cewa bindigar da aka samo a gidansa mallakinsa ce duk da cewa lasisin ta ya ƙare tun watan Disamba na shekarar 2021.

Kotun ta amince da gabatar da dukkan bayanan murya da sauran takardun da aka samo daga na’urorin sa a matsayin hujja, ciki har da bayanan wasu mutane da suka rubuta bayanai game da irin halin da suka shiga lokacin da aka yi garkuwa da su, duk kuwa da cewa ba su da ƙwarin gwiwar sake bayyana a gaban kotu saboda tsoro da tashin hankali da suka fuskanta.

Mai shigar da kara ya sanar cewa a zaman gaba zai nemi kotu ta kai ziyara ga ma’ajiyar dukkan kayayyakin da aka kwato, inda mai shari’a Umar ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe domin cigaba da sauraron karar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here