Matar dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC, Oluremi Tinubu, ta shawarci ‘yan Najeriya su fatattaki Mijinta daga gadon mulki bayan shekaru hudu idan har aka zabe shi bai yi abinda ya dace ba.
Matar Tinubu ta yi wannan furuci ne a Ralin mata na tallata Tinubu/Shettima a shiyyar kudu maso gabas wanda ya gudana a Owerri, babban birnin jihar Imo.
“Mu jingine batun addini a gefe, ni kirista ce shin kun taba tunanin watarana za’a jaraba tikitin Kirista da Kirista? Wai me asalin zancen ne, mun taɓa jaraba Musulmi da Musulmi to ku bari mu ƙara jaraba wannan.”
“Kuma bayan shekaru hudu, idan har ba su kawo sauyi mai kyau ba, zaku iya canza su daga kan mulki,” inji mai dakin Tinubu.
Sanatar ta bayyana cewa bai kamata a zaben Najeriya a tsaya ana kace-kace kan imanin mutane ba, kamata ya yi mutane su natsu su ɗauki dan takara mai tsoron Allah.
“Idan kuka samu mutum mai tsoron Allah, ba wai Kirista, Musulmi ko Katolika ba, mai tsoron Allah. Idan mai tsoron Allah ne a gadon mulki zai muku abinda ya dace.”













































