Gwamanatin tarayya ta ce zata kammala kashin farko na aikin titin Kano zuwa Katsina kafin karshen wannan shekarar.
Ministan aiki da gidaje, Umar El-Yakub, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya kai Kano ranar Asabar.
Ya ce an fitar da aikin tun a shekarar 2013, ya kara da cewa kammala aikin na daya daga cikin nasarorin da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu.
El-Yakub ya kuma yi kira ga ‘yan Kwangilar da su yi kokari su kammala gadar Yakasai -Badume, da zarar damuna ta wuce.













































