Gwamnatin tarayya ta amince da fara aiwatar da gwajin miyagun ƙwayoyi na dole kafin ɗaukar aiki ga duk masu neman shiga aikin gwamnati a faɗin ƙasa.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Sanarwar, ta bayyana cewa matakin ya zo ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin rage yawaitar amfani da miyagun ƙwayoyi da illolinsu ga ci gaban ƙasa, tsaro da ingancin aiki.
Sanarwar ta nuna cewa an fitar da wata takardar umarni ta bai ɗaya daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya zuwa ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sassan da ba na ma’aikata ba, domin aiwatar da sabon tsarin.
Ta wannan umarni, an umurci manyan sakatarorin ma’aikatu da shugabannin hukumomi da su sanya gwajin miyagun ƙwayoyi a matsayin wajibi a duk wani aikin ɗaukar sabbin ma’aikata.
Haka kuma, ta buƙaci ma’aikatun gwamnati da su yi aiki tare da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA wajen gudanar da gwaje-gwajen, bisa ƙa’idoji da hanyoyin da aka tanada.
Imohiosen ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon damuwa kan yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa, wanda ke da mummunan tasiri ga lafiyar jama’a, tattalin arziƙi, ingancin aiki da tsaron ƙasa, inda matakin ya yi daidai da aniyar gwamnatin da ke kan mulki na kare martabar ma’aikatan ƙasa.
NAN










































