Shugaban kwamitin tsaro na unguwar Faruruwa da makwabtan ta a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano, Yahaya Bagobiri, ya roƙi gwamnati ta tarayya da ta jiha da su gaggauta ɗaukar mataki kan tabarbarewar tsaro a yankin.
Bagobiri ya yi wannan roƙo ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a Faruruwa da sauran kauyuka makwabta.
Ya ce tun daga shekarar 2022 al’ummomin yankin ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke shigowa daga jihar Katsina da wasu unguwannin da ke makwabtaka da su, abin da ya jefa jama’a cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.
Shugaban ya bayyana cewa an rasa rayuka da dama, tare da sace dabbobi da dukiyoyi, ciki har da shanu, awaki da raguna fiye da 1,600, da kuma satar injuna da babura daga gonaki da gidajen mutane.
Ya kara da cewa kauyuka kamar Faruruwa, Kuraku, Goron-Dutse, Tsaure da Yan-Shado su ne suka fi fuskantar hare-haren, yayin da wasu mazauna yankin Tsanyawa suka tsere saboda yawaitar farmakin ‘yan bindiga.
Bagobiri ya ce ‘yan bindigar kan zo cikin daruruwan babura dauke da makamai, suna kai hari a kowanne lokaci na rana ko dare, lamarin da ya fi karfin jami’an tsaro kadan da ke yankin.
Ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da su karfafa rundunar tsaro a yankin domin kawo karshen matsalar da ta addabi al’ummomin Shanono da makwabta.










































