Asibitin AKTH da KEDCO sun sasanta rikici, an dawo da wutar lantarki

WhatsApp Image 2025 09 15 at 13.05.29 750x430 (1)

Asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya sanar da cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ya sake haɗa asibitin da layin wutar lantarki na ƙasa.

Wannan ya biyo bayan wata ganawa da aka gudanar tsakanin shugabancin asibitin ƙarƙashin jagorancinShugaban asibitin  Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe, da Daraktan KEDCO, Dokta Abubakar Shuaibu Jimeta, tare da kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori.

Tun da farko kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa KEDCO ta katse wutar lantarki a asibitin bisa rikicin bashin da ake bin sa wanda KEDCO ta bayyana cewa ya kai naira miliyan 949, yayin da AKTH ta ce nata ya tsaya a naira miliyan 880.

Labari mai alaƙa: AKTH, KEDCO suna musayar kalamai kan adadin bashi mai cin karo da juna da batun maido da wutar lantarki

A wata sanarwa da shugabar sashen yaɗa labarai na AKTH, Hauwa Inuwa-Dutse, ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa bayan ganawar, Daraktan KEDCO ya bayar da umarni ga injiniyoyin kamfanin su dawo da wutar lantarki zuwa asibitin ba tare da ɓata lokaci ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa lamarin ya warware cikin zaman lafiya da haɗin gwiwa tsakanin AKTH, KEDCO da kwamishinan ‘yan sanda na jihar.

Haka kuma shugabancin asibitin ya nuna godiyarsa ga kwamishinan ‘yan sanda da Daraktan KEDCO bisa goyon bayan da suka bayar a wannan lokaci mai wuya.

Shugabancin asibitin ya kuma sake jaddada aniyarsa na biyan dukkan bashin da ake binsa na wutar lantarki a matakin da ya dace.

Ya kuma gode wa jama’a bisa haƙuri da fahimtar juna da suka nuna a tsawon rikicin.

Asibitin ya tabbatar da cewa kiyaye lafiyar marasa lafiya da ci gaba da bayar da hidimar kiwon lafiya shi ne babban abin da ya fi mayar da hankali akai a kowane lokaci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here