Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rage hutun aikinsa na makonni biyu da ya ɗauka, inda ake sa ran zai dawo Abuja ranar Talata.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar mai taken: “Shugaba Tinubu ya kammala hutunsa kafin lokaci, zai dawo Abuja gobe.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban ƙasa ya kammala hutun nasa tun kafin wa’adin da aka tsara, kuma zai dawo Abuja a ranar Talata, 16 ga Satumba, 2025 domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati.
Tinubu ya tashi daga Najeriya zuwa ƙasar Faransa a ranar 4 ga Satumba, 2025 domin gudanar da wani ɓangare na hutun shekararsa.
An shirya farko cewa zai raba hutun tsakanin Faransa da Birtaniya kafin ya dawo gida.
A makon da ya gabata a birnin Paris, Shugaba Tinubu ya halarci liyafar sirri tare da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a fadar Élysée, inda suka tattauna muhimman fannoni na haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Faransa tare da amincewa kan zurfafa alaƙa domin ci gaban ƙasashen biyu da kuma zaman lafiyar duniya.
A sanarwar farko da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar 4 ga Satumba lokacin da ya fara hutun, an bayyana cewa Shugaba Tinubu zai yi hutun aiki a Turai na tsawon kwanaki 10, inda zai shafe wani ɓangare a Faransa sannan ya wuce zuwa Birtaniya kafin dawowarsa Najeriya.













































