WOFAN ta kaddamar da cibiyar kasuwanci a jihar Kano, tare da baiwa nakasassu 450 tallafi

WhatsApp Image 2025 03 01 at 01.00.01 1 750x430 (1)

Kungiyar nan mai rajin tallafawa mata a harkokin Noma (WOFAN) ta kaddamar da cibiyar tallafwa mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa nakasassu 450 tallafi.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa, wannan shiri na da nufin inganta sana’o’insu da kuma samar musu da kayan aiki irin nasu na nakasassu, da ba su damar yin ayyuka masu inganci da riba.

Da take jawabi a wajen taron a ranar Alhamis, shugabar shirin WOFAN-ICON2 ta kasa, Dakta Salamatu Garba, ta jaddada cewa cibiyar kasuwanci za ta baiwa mata damar sarrafa harkokin kasuwancinsu da kuma amfani da dabarun tattaunawa ta hanyar WOFAN.

Ta bayyana cewa, wannan shiri zai karfafawa mata ta hanyar ba su ikon sarrafa albarkatunsu, da kara samun riba, da kuma fadin albarkacin bakinsu kan batutuwan da suka shafe su.

Ta kara da cewa shirin ya yi daidai da manufofin shirin WOFAN-ICON2 a karkashin gidauniyar Mastercard, wanda ke kokarin samar da ayyukan yi mai dorewa ga matasa, mata, da nakasassu a jihohi goma na Najeriya. wanda shiri ne na tsawon shekaru biyar.

Karanta: Kungiyar WOFAN ta gano hanyoyin samar da wadataccen abinci a Najeriya

Da yake wakiltar ta jami’in kula da harkokin WOFAN na jihar Kano, Alhaji Dayyabu Abubakar ya jaddada cewa cibiyar ba wai kawai tana inganta hada-hadar tattalin arziki ba ne ta hanyar samar da ababen more rayuwa na kasuwanci har ma tana magance bukatu da dama na al’umma.

Ya kara da cewa cibiyar hada-hadar kasuwanci da aka bude a Karfi ita ce irinta ta biyu a karamar hukumar Kura, bayan da aka kafa irin ta a kasuwar Kura.

Kasuwar Kura, daya ce daga cikin manyan kasuwannin a Kano, tana sayar da hatsi sama da tireloli 500 a kullum zuwa wurare daban-daban a ciki da wajen Najeriya.

Ya kara da cewa cibiyar kasuwancin ta kunshi shaguna guda uku: daya yana aiki a matsayin ofishi inda mambobi zasu tattauna matsalolinsu da dabarun kasuwanci a cikin kasuwar Karfi, yayin da sauran biyun kuma an kebe su domin gudanar da kasuwanci.

Ƙaddamar da cibiyar tallace-tallace da abubuwan da ke da alaƙa da ita yana nuna ƙudurin WOFAN na ƙarfafa nakasassu, inganta dogaro da kai, da inganta rayuwa a tsakanin al’umma.

Hakimin Karfi, Alhaji Magaji Shehu wanda Jamilu Magaji ya wakilta ya taya wadanda suka ci gajiyar shirin murna, inda ya bayyana cewa shirin ba wai kawai zai amfanar da jama’a ba, zai kuma yi tasiri ga al’umma baki daya.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya tallafi wadanda suka ci gajiyar shirin tare da nuna godiya ga Dakta Salamatu Garba bisa yadda take tallafa wa marasa galihu.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin mai suna Hasiya Usaini da ke fama da nakasa, ta bayyana jin dadin ta da tallafin tare da bada tabbacin za ta yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace.

Ita ma wata wacce ta ci gajiyar tallafin, Rakiya Rabi’u ta yaba da tallafin, inda ta gode wa WOFAN da Dakta Salamatu Garba bisa yadda suke ci gaba da tallafa wa al’ummar Kura.

Hakazalika, Sule Shehu Abdullahi ya amince da kokarin WOFAN na taimaka wa nakasassu tare da bayyana kwarin gwiwarsa na amfanar shirin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here