Kotun Birtaniya za ta yanke wa Ekweremadu da matarsa hukunci a yau

Ike and Beatrice Ekweremadu.
Ike and Beatrice Ekweremadu.

A yau ne kotun hukunta manyan laifuka da ke Old Bailey a Birtaniya za ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa ​​Beatrice Ekweremadu da wani likita hukunci akan laifin safarar sassan jikin dan adam.

Kotun ta sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda, inda ake sa ran yanke musu hukunci a karon farko a irin dokokin bauta ta zamani.

Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas.

An kai shi Birtaniya ne a shekarar data wuce domin  aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke birnin London.

Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai  daga baya ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da wasu likitoci a ƙasar ta Birtaniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here