Amurka ta gargaɗi China kan bai wa Rasha tallafi a yakin Ukraine

FB IMG 16767988053298389
FB IMG 16767988053298389

Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce ya gargaɗi China cewa za ta ɗandɗna kuɗarta idan har ta bai wa Rasha wani taimako a yaƙin da take a Ukraine.

Mista Blinken ya bayyana haka ne a wata ganawa da babban jami’in diflomasiyyar China, Wang Yi a wani ɓangare na taron tsaro a Munich.

Da yake magana daga bisani, Mista Blinken ya ce Amurka ta samu bayanai cewa China na duba yiwuwar samar wa Rasha makamai abin da ya ce zai janyo babbar matsala ga alaƙarsu.

Jami’an biyu sun kuma yi magana kan balan-balan ɗin da aka kakkaɓo daga North Carolina a farkon watan nan.

Mista Blinken ya gargaɗi China da kada ta sake ta sake keta sararin samaniyar Amurka yayin da Wang Yi kuma ya ce Amurka ta gurgunta alaƙarsu saboda matakin da ta ɗauka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here