Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tono gawar marigayi mawakin nan, Mohbad domin a gudanar da bincike a kan gawar marigayin.
SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin a yammacin ranar Alhamis. Kakakin rundunar ‘yan sandan Legas ya kuma tabbatar da cewa an fara gudanar da bincike don gano yadda lamarin ya faru a sanadiyyar mutuwar matashin.
‘Yan sanda sun kuma kama ma’aikaciyar jinya da ta yi wa Mohbad magani kafin mutuwarsa.
Ana sa ran tawagar binciken za ta mika rahoton wucin gadi cikin makonni biyu.













































