Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya roki shugaban sa, Godwin Obakeki, da ya yafe musu sabanin da ke tsakaninsu a siyasance.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis a birnin Benin, Shaibu ya roki Gwamna Obaseki da ya yafe kuma ya manta.
“Ina amfani da wannan kafar don yin kira ga Maigirma Gwamna, idan akwai wani abu da ban san na yi ba, don Allah a gafarta mini domin mu ci gaba da bunkasa jiharmu tare,” inji shi.
“Muna da saura shekara guda. Mun kasance masu kishin kasa baki daya. Don haka mai girma gwamna, idan akwai wani abu da ka ji da na yi, don Allah ka yi hakuri. Ina bukatar mu yi aiki tare don gamawa da kyau da karfi. “