Gwamnatin Kano Ta Zargi NNPP Da Shirya Magudi A Zaben Gwamna

KATINEN ZABE
KATINEN ZABE

Gwamnatin Jihar Kano na zargin jam’iyyar adawa ta NNPP da shirin amfani da jami’an sa ido na bogi da nufin yin magudi a zaben gwamna da ’yan majalisar dokokin jiha da za a gudanar ranar Asabar.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba, ya yi zargin cewa NNPP ta buga takardun sa ido kan zabe an bogi ga jami’an bogi sama da 150 da take shirin turawa rumfunan zabe a birnin Kano ranar Asabar.

Ya yi zargin cewa NNPP ta yi hakan ne da nufin ba wa jami’an bogi damar kaiwa ga muhimman abubuwa a cibiyoyin zabe domin samun damar yin magudi da kuma sayen kuri’a.

Don haka ya bukaci jama’a sa kai karar duk wanda suka gani da katin sa ido kan zabe na bogi ga jami’an tsaro, yana mai kira kuma ga jami’an tsaron da su dauki matakin da ya dace a kan sojojin gonar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here