Mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun Abuja ya ci tarar EFCC Naira Dubu 500 a ranar Talata saboda neman dage shari’a sau da dama a shari’ar Godwin Emefiele.
Emefiele, tsohon gwamnan Babban bankin Najeriya (CBN), na fuskantar tuhume-tuhume da suka haɗa da karya amana ta laifi, ƙirƙirar takardu na bogi, amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, haɗa baki domin aikata damfara, da kuma karɓar kuɗi ta hanyar yaudara yayin da yake kan mukaminsa.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta zargi Emefiele da karɓar kuɗi Dala Miliyan 6,230,000 ta hanyar yaudara, wanda aka ce an tanada ne domin masu sa ido kan zaɓen ƙasa da ƙasa na zaɓen shekarar 2023.
Har ila yau, EFCC ta zarge shi da arzuta kan su ta haram da wasu kamfanoni biyu, wato April 1616 Nigeria Ltd da Architekon Nigeria Ltd.
Sai dai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.
Mai shari’a Muazu ya yanke hukuncin tarar ne bayan EFCC ta kasa gabatar da shaida mai lamba PW13, DCP Edwin Okpoziakeo, a gaban kotu domin bayar da shaida kamar yadda aka tsara, lamarin da ya haifar da dage shari’ar.
Jami’in ‘yan sanda DCP yana cikin tawagar da ta gudanar da bincike kan Emefiele a zargin damfarar.
Tun da farko, lauyan EFCC, A.O. Mohammed, ya sanar da kotu cewa duk da an sanar da shaidan bukatar halartarsa a kotu, bai samu halarta ba saboda wasu tsare-tsaren gudanarwa.
Ya bayyana cewa hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta umurce shi da ya rubuta wasiƙa ga Sufeto Janar na ‘yan sanda domin neman izinin halartar DCP ɗin a kotu, kuma ya yi hakan cikin gaggawa.
Sai dai daga baya DCP ɗin ya sanar da shi cewa yana da wata shari’a ta kansa a wata kotu a Gwagwalada a cikin babban birnin tarayya, inda aka sa dokar riƙe kuɗinsa.
Don haka ya roƙi kotu da ta ba shi damar dage shari’ar domin ya samu gabatar da shaidan.
Sai dai lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya yi ƙaƙƙarfan adawa da wannan bukata.
Ya jawo hankalin kotu zuwa sashe na 396 (3) da (4) na dokar tafiyar da shari’ar laifi ta shekarar 2015, wadda ta takaita yawan dage shari’a zuwa sau biyar kacal ga kowanne ɓangare tun daga fara shari’a har zuwa yanke hukunci.
Ya bayyana cewa a wannan shari’ar, EFCC ta ringa dage ta har sau takwas, wanda ya saɓa wa tanadin doka.
Ya ƙara da cewa masu gabatar da ƙara sun zaɓi barin shaidan ya fifita harkar kansa a kan aikin hukuma.
Ya ƙara da cewa tun daga shekarar 2023 zuwa yanzu, kotu ta rika ba su damar dage shari’a sau takwas, don haka ya roƙi kotu da kada ta sake amincewa da wata dagewa.
A hukuncinsa, Mai shari’a Muazu ya amince da hujjojin ɓangaren kariya, amma ya bayyana cewa kotu na da ikon amincewa da dage shari’a idan hakan yana cikin muradin adalci.
Ya ce mai bincike bai kamata a hana shi shiga cikin irin wannan shari’a ba.
Sai dai ya ci EFCC tarar Naira Dubu 500 saboda jinkirta shari’ar duk da cewa an amince da sauraron ta cikin gaggawa.
Daga bisani, mai shari’ar ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga Afrilu domin ci gaba da sauraro.












































