![Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin jihar Kuros Riba ta tsige... Rt. Hon. Elvert, Ekom, Ayambem, kuros, riba, tsige, kakakin, majalisar](https://solacebasehausa.com/wp-content/uploads/2024/05/Rt.-Hon.-Elvert-Ekom-Ayambem-696x399.jpg)
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
An tsige Rt. Hon. Elvert Ekom Ayambem a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Kuros Riba.
A ranar Laraba ne ‘yan majalisar 17 suka tsige shugaban majalisar bisa zargin karkatar da wasu kudade.
Karin labari: Gwamnan Kano ya nemi haɗa kai da kasar Netherland kan habaka noma da dakile illolin sauyin yanayi
An gabatar da kudirin tsige Hon. Effiom Ekarika mai wakiltar mazabar Calabar South da Hon. Omang Charles Omang mai wakiltar mazabar jihar Bekwarra.
An zabi Rt. Hon. Elvert Ayambem shugaban majalisar dokokin jihar Kuros Riba ta 10 a watan Yunin 2023.
Ayambem yana wakiltar mazabar Ikom a majalisar dokoki.
Karin bayani na tafe…