Uwargidan shugaban Najeriya, Hajiya A’isha Buhari isa cikin zauren majalisar dattawa.
Ziyarar da A’isha ta kai zauren majalisar a ranar Laraba ta tarihi ce, domin a cewarta ita ce matar shugaban kasa ta farko da aka karbi bakunci a zauren majalisar dattawa.

Majalisar dattijai ta dage gabatar da rahoton zuwa wani lokaci a yayin gudanar da aikin domin baiwa Misis Buhari damar zuwa.
Ta samu rakiyar ministar harkokin mata Mrs Pullen Tallen; Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Mrs Zainab Ahmed da wasu mataimakanta.













































