Jam’iyar ADP ta nada tsohon shugaban jam’iyar APC Engr. Bashir Yahaya Karaye a matsayin shugaban riko na jam’iyyar ADP a Kano.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kano Bashir Karaye ya ce shalkwatar jam’iyyar ta kasa ce ta tabbatar da nadin nasa a ranar 16 ga watan Satumban 2022 kuma an rantsar da shi a ranar.
Cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Kano a Jami’ayar Abbas Yushau Yusuf ya fitar, ta ce shugaban rikon hazikin dan siyasa ne tun zamanin jamhuriya ta biyu, ya ce zai hada kai da dan takarar gwamna na jam’iyyar a Kano Shaaban Ibrahim Sharada don tabbatar da tsarin dimokuradiyya na gaskiya kuma mai inganci a cikin jihar.
“Karaye wanda ya kasance Sakatare kuma memba a jam’iyyun siyasa daban-daban a Kano tun farkon jamhuriya ta hudu, ya ce jam’iyyar ADP za ta gudanar da duk wani salon mulkin da bai saba doka ba ko kabilanci, jinsi ko bangaranci ba,” in ji sanarwar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Bashir Yahaya Karaye ya kasance kwamishina a gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje.
Injiniya Bashir Yahaya Karaye ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar ADP da su koma unguwanninsu dan su yi rajista, su karbi katin zama mambobi a Jam’iyar.
‘’Cikin wasikar nadin da shugaban jam’iyyar na kasa Injiniya Yabagi Sani ya aikewa sabon mukaddashin shugaban jam’iyyar ADP a Kano, ya bukaci Karaye da ya daidaita kwamitin zartarwa na jihar Kano wanda zai rika yadawa tare da tabbatar da dukkanin sassan jihar sun samu wakilci.













































