Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jalingo babban birnin Jihar Taraba, ta soke zaben fidda gwanin takarar gwamnan Jihar da ya bawa Sanata Emmanuel Bwacha, damar zama dan takarar a zaben 2023.
A ranar Talata ne alkalin kotun mai shari’a Simon Amobeda, ya yanke hukunciaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaakan karar da daya daga cikin ‘yan takarar gwamnan, David Kente, ya shigar gabanta bisa zargin rashin sahihancin zaben.
Alkalin kitun ya umarci hukumar zabe ta Kasa INEC da ta gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna a jihar nan da kwanaki 14.
Amobeda, ya kuma umarci Bwacha, da ya daina bayyana kansa a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, haka kuma INEC kar ta Kara amincewa da Bwacha a matsayin dan takara.
Muna tafe da Karin bayani…………













































