Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Jigawa Alhaji Salisu Zakar ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Auwalu Danladi Sankara ne ya tabbatar da rasuwarsa.
Ya ce, “Muna sanar da rasuwar dan majalisar zartarwa ta jihar Jigawa, Salisu Zakar, kwamishinan kasuwanci da masana’antu.
Kafin rasuwarsa, Salisu Zakar ya yi aiki a jihar Jigawa a wurare daban-daban, tun daga ma’aikacin gwamnati, ya zama shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar (wato SUBEB), sannan kuma ya zama kwamishinan kasuwanci da masana’antu.
Ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano (wato AKTH), da ke jihar Kano bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
Marigayi Zakar wanda ya rasu yana da shekaru 60 a duniya, ya bar matansa, da ‘ya ’ya, da jikoki.













































