Gwamnatin tarayya ta ce ba ta da isassun kudaden da za ta biya wa Kungiyar Malaman Jami’o’I ta kasa ASUU bukatunta domin ta janye yajin aikin da take yi kusan watanni shida, a kasar nan.
Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, ya ce gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta da wani abin da zai hana kungiyar Malaman Jami’o’in (ASUU) ci gaba da gudanar da yajin aikin.
Mista Keyamo, wanda ke magana a wani shirin gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, ya ce shawarar da ya baiwa iyayen daliban jami’a shi ne su roki ASUU domin su janye yajin aikin da suka kwashe watanni a cikinsa.
“Zan gaya wa iyaye da kowa; ku je ku roki ASUU,” inji shi.
Kungiyar ASUU dai ta dage cewa ta cimma matsaya da kwamitin da gwamnatin Buhari ta kafa kuma abin da ake bukata shi ne bangarorin su sanya hannu tare da warware matsalolin.
Sai dai gwamnatin tarayya ta gaza rattaba hannu kan yarjejeniyar domin ta sasanta da kungiyar ASUU.
A yayin da gwamnatin Buhari ke ci gaba da ikirarin rashin samun isassun kudade don magance bukatun malamai, sau da yawa takan sanya abubuwan da basu da fifiko cikin kasafin kudi.
A cikin watan Afrilu, shugaba Buhari ya ba da gudummawar dala miliyan 1 ga gwamnatin Taliban ta Afganistan a matsayin taimakon agajin jin kai.
Kazalika a watan Yunin da ya gabata ma, gwamnatin ta kashe sama da Naira biliyan 1 wajen sayo manyan motoci ga gwamnatin Jamhuriyar Nijar.