Tsohon gwamnan jihar Plateau Joshua Dariye da takwaransa na jihar Taraba Jolly Nyame sun shaki iskar ‘yan ci, ya yin da aka sake su daga gidan ajiya da gyaran hali na Kuje dake garin Abuja.
Idon za’a iya tunawa dai wata biyar da suka wuci, 14 ga watan Afrilu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amunci da yi musu afuwa.
Wani shaidar gani da ido daga gidan gyaran halin ya shaidawa jaridar Dail Trust cewa tsofafin gwamnonin an sake su ne da misalin 2:15pm a yau Litinin.
Ya yin da ake tun tubar maimagana da yawun gidan gyaran halin, Chukwuedo Humphrey, ya tabbatar da sakin na su.













































