Majalisar dokokin Kano zata binciki dalilan koma-bayan da Kano Pillars ta samu a gasar wasannin NPFL

kano pillars 1 1
kano pillars 1 1

Majalisar Dokokin Kano Zata binciken Dalilan koma-bayan da Kano Pillars ta samu Agasar wasannin NPFL.Majalisar dokokin jihar Kano ta umurci kwamitin ta mai kulada harkokin wasanni da ya binciki musababbin ficewar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars daga gasar wasannin kwallon kafan firimiya ta Najeriya NPFL.

Hakan na kunshene biyo bayan amincewa da kudirin Wanda Dan majalisa dokoki Alhaji Nurudeen Alhassan Mai Wakiltar rano ya gabatar yayin zaman majalisar na ranar Litinin.

Cikin kunshin kudirin, Alhassan, wanda kuma shine shugaban kwamitin riko na majalisar, ya bayyana wasanni a matsayin ginshikin ci gaban matasa.

A cewarsa, ficewar Kano Pillars daga gasar wasannin firimiyar wani al’amari ne mai ban ta’ajibi wanda dole ne a yi bincike matuka don hana afkuwar lamarin nan gaba.

Majalisar ta amince da kudirin baki daya, sannan ta bukaci kwamitin da ke kula da harkokin wasanni da ya gudanar da bincike tare da bayar da rahoto cikin makonni biyu domin ci gaba da aiwatar da dokar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here