Nana Akufo-Addo, ya nesanta kansa da wani rubutu da aka yi zargin ya wallafa a shafinsa na Facebook game da Tinubu da Peter Obi

images 15 569x430 1
images 15 569x430 1

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya nesanta kansa da wani rubutu da aka yi zargin ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda yake shawarta Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, da ya baiwa Peter Obi dama.

A wani sako da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Talata, Akufo-Addo ya ce nemawa Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) dama a wajen Tinubu, karya ne kuma ba shi ne ya wallafa ba.

Shugaban Ghana ya ce shi bai yi irin wannan rubutun ba kuma ba zai taba tsoma baki cikin harkokin cikin gida da siyasar Najeriya ba.

“An jawo hankalina ga wani rubutu mai tayar da hankali da ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, inda ake zargin na rubuta wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, cewa a baiwa Peter Obi dama ya nemi magani ga lafiyarsa”.Akufo-Addo ya rubuta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here